Ministan Wutar Lantarki, Adelabu Adebayo, ya bukaci ‘yan kasa da su nuna kishin kasa a duk lamuransu musamman kan kadarorin kasa.
Adelabu ya yi wannan kiran ne a sakonsa na sabuwar shekara ta wata sanarwa da Bolaji Tunji, mashawarcinsa na musamman kan harkokin sadarwa da hulda da manema labarai ya fitar.
Ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ake yawan kai hare-hare da barnata turakun wutar lantarki.
Ya danganta harin da ake kai wa akai-akai, wanda ya ce ya yi illa ga karuwar samar da wutar lantarki ga gidaje da ‘yan kasuwa.
A cewarsa, babban abin da ya kawo cikas ga samun nasarar samar da wutar lantarki a kasar nan a shekarar da ta gabata, shi ne, hannun wasu ‘yan kasa marasa kishin kasa ne wadanda suka bayyana a matsayin ‘yan bindiga.