Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar ya bude wani taron shugabannin tsaro na kungiyar ECOWAS karo na 43 a Abuja, domin karfafa kawancen tsaro wajen tinkarar matsalolin ta’addanci, da aikata laifuka da matsalolin sauyin yanayi.
A jawabinsa na budewa, Badaru ya jaddada bukatar gaggauta magance matsalolin tsaro dake addabar yankin Sahel da afirka ta yamma.
Ministan yace batutuwan da aka tsara tattaunawa a taron zasu mayar da hankali kan matsayar ECOWAS, da ayyukan wanzar da zaman lafiya da kuma batun tsaron gabar tekun Guinea.
Ya bayyana kwarin guiwar cewa hadin guiwar zai samar da mafita kan matsalolin aka za’a tattauna tare da kawo managartan hanyoyin kawar da kalubalen tsaro a yankin.