Ministan Tsaro ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika ba jami’an tsaro bayanan sirri

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika ba jami’an tsaro bayanan sirri domin inganta tsaro.

A taron Gwamnati da Jama’a da aka yi a Birnin Kudu nan jihar Jigawa, Badaru ya ce fitar da bayanai na da muhimmanci wajen magance matsalar tsaro.

Ya yaba da yadda tsaro ya inganta karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa yaki da ta’addanci aiki ne na kowa da kowa.

Ministan ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa gagarumin ci gaba da aka samu cikin watanni 18 da suka wuce a Jigawa.  

Comments (0)
Add Comment