Kamfanin bada shawara kan harkokin kuɗi da haraji, KPMG ya yi hasashen matsalar rashin aikin yi a Najeriya za ta ƙaru zuwa kashi 40.6 cikin 100 idan aka kwatanta da matakin da ta kai bara, wato kashi 37.7 cikin 100.
KPMG ya bayyana haka ne a rahotonsa da yake fitarwa kan tattalin arziki inda a ciki ya ce “matsalar rashin aikin yi za ta ci gaba da zama babban ƙalubale a 2023 saboda rashin zuba hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu da ƙarancin masana’antu da rashin bunƙasar tattalin arziki kamar yadda ya kamata da kuma kasancewar tattalin arzikin Najeriya ba zai iya samar wa mutum miliyan 4 zuwa 5 aikin yi ba duk shekara.”
Rahoton ya kuma bayyana cewa ana fatan ma’aunin tattalin arzikin Najeriya, GDP zai ci gaba da samun tagomashi da kashi 3 cikin 100 a 2023 sai dai cikin yanayi irin na tafiyar hawainiya saboda yanayi na miƙa mulki a ƙasar.
Kamfanin ya kuma yi hasashe cewa ɓangaren sadarwa da harkokin kasuwanci da kuma ɓangaren mai za su farfaɗo sanadin matakan da ake ɗauka na magance matsalolin tsaro.