Matsala: Hukumar agajin gaggawa ta yi hasashen samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 12 a Jigawa

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa tayi hasashen samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 12 na jihar Jigawa.

Jami’in hukumar mai kula da ofishin hukumar na shiyyar Kano, Sanusi Ado ya bayyana haka a lokacin gangamin wayar da kan alumma kan matakan kariya daga ambaliyar ruwa a Dutse.

Jami’in wanda ya samu wakilcin mataimakin darakta a hukumar, Aminu Boyi Ringim, yace kananan hukumomin da ake hasashen samun ambaliyar ruwan sune Ringim da Kaugama da Taura da Guri da Gwaram da Dutse da Auyo da Miga da Malam-Madori da Birniwa da Jahun da kuma Kafin Hausa.

Sanusi Ado ya kara da cewa sun ziyarci jihar Jigawa ne domin wayar da kan alumma kan matakan kare kai daga ambaliyar ruwan da ake hasashen samu a bana.

Tun da farko a jawabinsa sakataren zartarwa na hukumar bada agajin gaggawa ta jiha, Yusif Sani Babura, ya godewa hukumar bisa zabar jihar Jigawa domin gudanar da gangamin wayar da kan.

NEMA
Comments (0)
Add Comment