Matasan Yobe Sun Bukaci Jajircewa Kan Makomarsu

Matasa a Damaturu sun bukaci gwamnatin jihar Yobe da ta karfafa shirin samar da ayyukan yi wajen raba su da zaman kashe wando.

Da yawa daga cikinsu wadanda suka tattauna da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, sunce shirin samar da aikin shine babbar hanyar dogaro da kai da habaka tattalin arziki.

Wani matashi marar aikin yi, Abubakar Yusuf, yace akwai tsammani sosai daga matasa ga gwamnatin Mai Mala Buni.

Haka kuma wani matashin mai suna Usman Mohammed, yace guraben aikin da ba a cike ba a ofisoshin gwamnati, sunyi kadan, a saboda haka gwamnati ta mayar da hankali wajen bayar da horo da koyarda sana’o’i ga marasa aikin yi. A nasa bangaren, Musa Kallamu, yace matasa a shirye suke su shiga aikin noma da kiyo domin habaka tattalin arzikinsu.

JOBYOBEYOUTH
Comments (0)
Add Comment