Rundunar sojin Najeriya ta ce ana samun ƙaruwar matasan kasar da ke shiga ayyukan rashin tsaro, sanadiyyar matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.
Daraktan watsa labarai na rundunar sojin Najeriyar Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya shidawa BBC hakan yayin wani taron bikin cika shekara guda da hafsan tsaron ƙasar Christopher Musa ya yi a kan karaga.
Birgediya Janar Gusau ya ce wannan matsala na maida hannun agogo baya a yaƙin da ake yi da matsalolin tsaro a sassan ƙasar baki daya.
Ya ce yawanci matasan da ke ɗaukar makaman saboda matsin rayuwa a yankin arewacin ƙasar suke, inda ake ta fafutukar kawo karshen ayyukan yan bindiga da masu satar mutane don neman fansa
A cewarsa ”Bai kamata matashi ya shiga irin wannan aiki na saba doka ba sabida wani hali da ya tsinci kansa a ciki”
Ya kara da cewa ƙarin wata matsala da suke fama da ita, ita ce ta ƙarancin makamai da kayan aiki, ko da yake gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta wajen warewa ɓangaren tsaro kudi mai tsoka, amma duk da haka bai wadatar ba
Sai dai duk da irin waɗannan matsaloli, kakakin Janar Gusau ya ce an samu nasarori da dama a shekara guda ta farko da shugaban rundunonin tsaron ƙasar ya yi a kan mulki.
A cewarsa “A bara hanyar da ta Abuja zuwa Kaduna, kusan kullum sai ka ji an yi garkuwa da mutane, amma yanzu saboda matakai da muke dauƙa an magance wannan matsala, mutane na bin hanyar ba tare da wata fargaba ko matsala ba”
Ya ƙara da cewa “Idan ka je ta arewa maso gabas an samu sauyi, idan aka kwatanta da bara, haka abun yake a arewa maso yamma”
Sai dai ya ce duk da haka akwai sauran matsalar, don haka za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin kare ƴan Najeriya da dukiyoyinsu ko a ina suke.
Har yanzu dai matsalar tsaro na ciwa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya, kuma duk da kokarin da gwamnatin kasar ke cewa tana yi wajen shawo kan matsalar, har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin jihohi kamar su Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Neja, har yanzu ‘yan fashin daji na ci gaba cin karensu ba babbaka.
Ko da a farkon watan nan na Yuni, wasu ƴan majalisar wakilan kasar na Arewa, inda aka fi fama da matsalar sun tayar da jijiyar wuya, suna kiran a sauya salon yadda ake yaƙi da matsalar, domin a ganinsu babu wani sauƙi da ake samu.
‘Yan majalisar sun ce duk da cewar bangarorin da ke yaki da matsalar tsaron na aiki tare, amma akwai bukatar samun fahimtar juna musamman a bangaren shugabannin siyasa, watau gwamnonin jihohi da kuma gwamnatin Tarayya, ta yadda za a yi wa lamarin taron dangi.