Biyo bayan tsammanin da ake dashi na barin baki suyi Umrah a kasar Saudi Arabia cikin wannan shekara, Hukumar Aikin Hajji, ta kasa bukaci masu sha’awar zuwa Umrah, su tabbatar da cewa sun kiyaye da dokokin da Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta shinfida a kasar.
Hukumar ta NAHCON ta ce sharadan da Ma’aikatar da gindiya dole ne a bi su domin a lokacin da ake gudanar da Ibadojin.
Sanarwar da Ma’aikatar ta fitar ta nuna cewa baki masu sha’awar zuwa Umrah a bana sun fara samun Biza daga ranar 25 ga watan Yuli, inda kuma zasu fara shiga Saudi Arabia daga ranar 9 ga watan Agustan da muke ciki.
Kazalika sanarwar ta bukaci masu sha’awar zuwa kasar su tabbatar da cewa sunbi umarnin da gwamnatin kasar ta sanya domin kaucewa faruwar lamarin.