Masu Neman Aikin Dansanda 8,062 Ke Halartar Tantancewa A Jigawa

Rundunar Yansandan Jahar Jigawa tace a kalla masu neman aikin Dansanda 8,062 ne suke halartar aikin tantancewa domin daukar su aikin dansanda.

Jami’in hulda da jama’a a rundunar, Sufritanda Abdu Jinjiri ne ya bayyana hakan ga menama labarai a Dutse cewa an zabo masu neman aikinne daga dukkanin Kananan Hukumomi 27 dake Jahar.

Abdu Jinjiri ya bayyana cewa aikin tantancewar na tsawon kwanaki 28 wanda aka fara ranar 1 ga watan Yuli, yana gudana ne karkashin rundunar da kuma hukumar kula da ayyukan Yansanda ta Kasa.

Ya kara da cewa a yayin tantancewar, zasu bincika lafiya da kuma takardun masu neman aikin. Ya ce kawo jiya Laraba, mata 2 ne kadai daga cikin masu neman aikin 8,062 suka halarci tantancewar.

JigawaPolicepolicemen
Comments (0)
Add Comment