Masarautar Kazaure da ke nan jihar Jigawa ta raba zakkar hatsi da dabbobi na sama da Naira miliyan 8 da dubu dari 5 ga marasa galihu dubu dari 220 da 12 a yankin.
Mai magana da yawun masarautar Gambo Garba ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN a ranar Asabar.
Malam Garba ya ce shugaban kwamitin tattarawa da rabon zakka na majalisar masarautar, Bala Muhammad ne ya bayyana hakan a taron raba zakka a gundumar Amaryawa.
Ya kara da cewa an raba zakka mai kunshe da dabbobi da hatsi ga iyalai da suka cancanta a yankin Yankewa Tuntube dake gundumar Amaryawa a ranar 1 ga watan Janairun 2023.
Kakakin ya kara da cewa, Muhammad ya danganta nasarar da kwamitin ya samu a yayin gudanar da rabon bisa goyon baya da hadin kai da suka samu daga majalisar masarautar.
A cewarsa, Sarkin Kazaure, Alhaji Najeeb Hussaini, ya yi kira ga masu hannu da shuni a yankin da su ci gaba da bayar da Zakka domin tallafa wa marasa galihu da masu karamin karfi a cikin al’umma domin rage radadin talauci.