Makasudin Hana Hawan Sallah a Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, ya soke gudanar da bukuwan sallah babba dake tafe, tare da haramtawa sarakunan jihar 5 gudanar da hawa.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne, yayin ganawa da yan Jaridu a Dutse, babban birnin jihar, inda yace hakan nada alaka da kokarin gwamnatin jihar, na cigaba da yakar annobar alakakai ta corona.

Tare da bayyana shafe sama da wata guda ba tare da samun mai dauke da cutar a jihar ba, a matsayin nasara.

Yace duk da irin nasarori da aka samu a yaki da annobar, gwamnati ba zatayi kasa a gwiwa ba, wajen cigaba da daukar matakan dakile cutar.

Ya kuma ce tuni manyan tireloli kimanin 110 cikin guda 150 suka iso makare da kayayyakin abinci jihar, inda aka aike da kowacce tirela daya, ga masu amfana kai tsaye.

Ya bada tabbacin cewa, rabon kayan abincin ya wakana a dukkanin mazabun jihar 287, dake kananan hukumomin jihar 27.

Sannan ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu, kasancewar karin kayayyakin jin kan na tafe.

JigawaMuhammad Badaru AbubakarSallah Festival
Comments (0)
Add Comment