Majalisar wakilan Najeriya na duba yiwuwar tilasta bai wa mata sojoji damar sanya hijabi

Majalisar wakilan Najeriya na tattaunawa a kan wani ƙuduri da aka gabatar a gabanta, da ke neman bai wa sojoji mata da takwarorinsu da ke aiki da ƙungiyoyin tsaro a ƙasar damar sanya hijabi idan suna da sha’awa.

Ɗan majalisar da ya gabatar da ƙudurin Saidu Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ya gabatar da shi ne don ganin yadda sanya hijabin ke neman zama wani abin muhawara a Najeriya duk da doka ta bayar da damar sanyawa.

Sai dai ya ce ”Ba wai muna maganar Musulunci bane kawai, wannan ƙuduri ya kuma nemi a bada kariya ga dukkan masu bin addinai, don haka ba wai maganar hijabi ba ce ƙadai a cikinsa, don mun san cewa ba Musulmai ne kadai ke fama da matsalar nuna musu wariya ba, har da Kiristoci ma suna fama da wannan matsala, wasunsu ma ba sa iya yin magana”

Ya ƙara da cewa ”akwai wurin da ƙila Kirista zai iya samun kanshi da wataƙila Musulmai ne ke da rinjaye kuma shima ya gamu da irin wannan matsala, don haka wannan kuduri zai sama masa kariya shi ma” in ji ɗan majalisar

A halin da ake ciki dai ƙudurin ya tsallake karatu na biyu, kuma majalisar wakilan za ta ci gaba da tattaunawa a kai kafin a kai ga amincewa da shi idan hali ya yi.

Abin da ƙudurin ya ƙunsa

Sashe na 13 na kudirin na neman a hana rundunar soji da dukkan wasu ƙungiyoyin tsaro masu zaman kansu a Najeriya cusguna wa duk wani jami’a da ya zabi sanya hijabi a bakin aiki.Har ila yau ya kuma sashe na 13, 2 cikin baka na wannan ƙuduri ya buƙaci rundunar soji a Najeriya ta samar da wata kariya ta musamman ga duk wani jami’i da ya zaɓi gudanar da al’amuransa dai dai da tsari da manufa, da kuma koyarwar adinin da yake bi.

Ƙudurin mai taken – Dokar bada kariya da hana tsangwama da nuna banbancin addini bai tanadi wani hukunci da za a iya yankewa duk wanda ya saɓa shi ba, ko da yake ya bayyana yin hakan a matsayin aikata laifi da za a iya hukunta mutum a kai.

Yadda batun sanya hijabi ke tada ƙura a Najeriya

Batun sanya hijabi a Najeriya dai na ci gaba da tada ƙura musamman a kwanakin nan a Najeriya, harta kai ga rufe makarantu da haifar da tashin hankali tsakanin mabiya addinin musulunci da kuma na kirista.

Rikici na baya banan nan shine wanda aka samu a Illorin dake jihar Kwara, wanda ta kai har gwamnatin jihar ta rufe wata makaranta saboda hana dalibai musulmai sanya hijabi.

Doka a Najeriya ta bada damar sanya hijabi, sai dai hakan ya gamu da tirjiya daga wasu masu makarantun kiristoci dake ganin cewa tsarinsu ya sha ban ban da na mabiya addinin islama.

Kungiyoyin addinin musulunci na ci gaba da kiran a bawa musulmai damar sanya hijabin a ko ina, yayin da takwarorinsu na kiristoci ke cewa yawancin makarantun da ke hana sanya hijabin na kiristoci ne waɗanda tsarinsu ya sha ban ban da na musulunci.

Asalin Labarin: https://www.bbc.com/hausa/labarai-56685126

Comments (0)
Add Comment