Majalisar wakilai ta kasa za ta gudanar da zama a gobe domin gyaran dokar zabe ta 2022.
Magatakardar majalisar, Yahaya Danzaria, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau yace ‘yan majalisar za su zauna domin gyaran wani babban kuskure a dokar.
Tunda farko, majalisar dattawa ta gyara sashe na 84, karamin sashe na 8 na dokar zaben, domin bayar da dama ga manyan deliget suyi zaben cikin gida.
Kudirin, wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya gabatar, an zartar da shi yayin zaman majalisar.
A dokar zaben da ake da ita a yanzu, ba a bayar da dama ba ga manyan deliget.
Ovie Omo-Agege ya ambaci manyan deliget da suka hada da shugaban kasa da mataimakinsa da ‘yan majalisun tarayya da gwamnonin jihoshi da mataimakansu.