Majalisar Legas ta yi Alla-wadai da sakin ƴan Arewa 123 da aka kama a jihar

Majalisar dokokin jihar Legas ta yi Alla-wadai da sakin ‘yan asalin jihar Jigawa 123 da hukumar tabbatar da tsari a jihar ta kama yayin da suke shiga jihar.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Honarabul Sanai Agunbiade, ne ya taso da maganar yayin zaman majalisar na ranar Alhamis. Sanai ya ce babu wanda ya san mene ne nufin mutanen da suka shigo jihar da babura masu yawa, ya bayyana hakan a matsayin babbar barazana ga tsaro a jihar.

‘Yan majalisar sun koka a kan yadda yaran Hausawa ke tururuwar shiga garin Legas da babura ko motoci cike da shanu tare da yin kira ga kwamishinan ‘yan sandan jihar a kan ya tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar mutanen garin Legas. Kazalika, majalisar ta yi kira ga majalisun tarayya da su sake yin duba na tsaki a kan kudirin bukatar kirkirar ‘yan sandan jihohi.

Honarabul Macauley Mojisola, mamba mai wakiltar mazabar Amuwo 1, ya ce akwai bukatar gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu, ya sanar da sauran gwamnoni a kan su sanar da mutanensu bukatar yin biyayya ga dokokin jihar Legas.

Wani mamba a majalisar, Fatai Mojeed, mai wakiltar mazabar Lekki 1, ya ce akwai bukatar hukumar kula da rijistar ababen hawa ta fara kamen baburan da basu da takardun rijista da gwamnatin jihar Legas.

Shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, ya ce yana goyon bayan abinda mambobin majalisar suka fada tare da bayyana cewa kasafin kudin jihar Legas ba zai isa adadin mutanen dake shigo musu ba.

ArewaLagos
Comments (0)
Add Comment