Majalisar Dokokin Jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus.
Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda.
Bayan murabus ɗin nata, nan take ‘yanmajalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Najeriya.
‘Yanmajalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayinmace ta farko kakakin majalisa.
Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar game da yadda za a shawo kan rikicin.