Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da mayar da shugabannin kananan hukumomin nan hudu da aka dakatar

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da mayar da shugabannin kananan hukumomin nan hudu da aka dakatar daga kan mukamansu na tsawon watanni.

Shugabannin kananan hukumomin da abin ya shafa sun hadar Baffa Shinge na karamar hukumar Auyo da Malam Bala Usman Chamo na karamar hukumar Dutse da Shehu Sule Udi na karamar hukumar Ringim da Ahmad Rufa’I na karamar hukumar Gumel.

Mayar da shugabannin kananan hukumomin guda hudu ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamatin wucin gadi da majalisar ta kafa domin gudanar da bincike akan shugabannin kananan hukumomin guda hudu.

Da ya ke gabatar da rahotonsa, mai rikon shugabancin kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa Alhaji Aminu Zakari ya ce kwamatin ya dauki kwararre mai binciken kashe kudade mai zaman kan sa dan gudanar da bincike kan yadda kananan hukumomin guda hudu ke kashe kudade inda aka same su da rashin bin ka’idoji wajen kashe kudade.

Ya ce kwamatin ya gana da shugabannin hudu wadda su ka nemi afuwar kwamatin tare da bada tabbacin aiki da ka’idojin kashe kudade domin cigaban kananan hukumominsu.

Bayan nuna goyon baya da gagarumin rinjaye kan rahoton kwamatin, daga nan sai shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da mayar da shugabannin kananan hukumomin guda hudu kan mukamansu.

Comments (0)
Add Comment