Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci manyan hafsoshin tsaron ƙasar

Majalisar Dattawan Najeriya ta sake buƙatar manyan hafsoshin tsaron ƙasar su bayyana a gabanta a mako mai zuwa, kan ƙaruwar matsalar tsaron ƙasar.

Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a lokacin zaman majalisar na ranar Laraba.

A baya dai majalisar ta gayyaci manyan hafsoshin tsaron, domin bayani kan matsalar tsaron ƙasar, sai dai ba su halarta ba, wani abu a Sanata Akpabio ya danganta da rashin samun lokaci.

Shugaban majalisar ya ce a mako mai zuwa manyan hafsohin za su bayyana a gaban majalisar domin bayar da bahasi kan manyan matsalolin tsaro da ke damun ƙasar da irin matakan da suke ɗauka domin magance su.

Waɗanda gayyatar ta shafa sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla da kuma babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar.

Sauran sun haɗa da Babban Sifeton ƴansanda, da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya.

Comments (0)
Add Comment