Majalisar wakilai ta kasa zata gana da ministoci da manyan jami’an gwamnati, domin amsa tambayoyi kan kudaden bashi da kasarnan ke karbowa daga ketare, musamman China.
Kwamatin majalisar na yarjejeniya, yayi kiranye ga ministar kudi, kasafi da tsare tsare, Zainab Ahmad, ministan Sadarwa da cigaban tattalin arziki ta yanar gizo, Dr. Isah Ali Pantami, sannan ministan wuta Sale Mamman, da ministan sufuri Rotimi Amaechi da kuma darakta janar ta ofishin dake kula da basuka, Patience Oniha da dai sauransu.
- Tchiani ya gabatar da kasafin kuɗin Jamhuriyar Nijar na 2025
- Gwamnatin Jigawa ta ware Naira miliyan 413 domin dakile matsalar tsaro a jihar
- Ministan Wutar Lantarki ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu alkinta kadarorin kasar
- Nuhu Ribadu ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na dakile barazanar tsaro
- An yiwa yara fiye da miliyan 10 rijistar haihuwa cikin watanni 3 a Najeriya
Shugaban kwamatin Mr Nicolas Ossai, ya shaidawa manema labarai cewa, wadanda aka aikewa da kiranyen, ana sa ran su bayyana gaban kwamatin a yau Litinin.
Tun dai a ranar 28 ga watan yulin da ya gabata ne, kwamatin ya soma bincike kan kudaden bashi da kasarnan ke ciyowa, wanda ta fara da bashin dala miliyan 500 da aka karbo daga China, domin aikin titin jirgin kasa.
Yan majalisa dai sun bara kan yarjejeniyar bashi da kasarnan ta rattaba hannu da China a kai, wanda sukace tamkar mika wuya ne ga kasar idan aka gaza biya.