Mai martaba sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussain Adamu ya hori mata musulmi da su kara tashi tsaye wajen neman ilmin addini da na zamani domin sanin yadda zasu bautawa Allah SWT.
Sarkin ya yi kiran ne a lokacin bikin saukar karatun dalibai 55 na makarantar Madarasatul Ummil Mu’umimina Aisha Islamiyya Kazaure.
Sarkin wanda ya samu wakilcin Iyan Kazaure, Alhaji Ummaru Tafida Adamu ya bukaci daliban da su yi kyakkyawan amfani da baiwar da Allah ya basu.
A nata jawabin shugabar makarantar Hajiya Zainab Umar Abdullahi tace makarantar ta na da yawan dalibai 280 da ajujuwa 9 da malamai 16.
A wani labarin kuma, kwamitin zakka na masarautar Kazaure ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da kudi da kuma dabbobi na kimanin kudi naira miliyan 4 da dubu 280 ga mabukata 826 a garin Firji na gundumar Achilafiya.
Shugaban kwamitin, Alhaji Bala Muhammad ya sanar da hakan a wajen rabon zakkar.