Mai martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje ya bukaci masu ruwa da tsaki a masarautarsa dasu hada hannu waje guda domin ciyar da masarautar gaba.
Mai Martaba ya yi wannan kiranne a lokacin taron tattaunawa da limaman masalatan juma’a dana kamsisalawati da masu unguwanni wanda kungiyar cigaban matasan masarautar Hadejia ta shirya.
Sarkin wanda ya samu wakilcin Turakin Hadejia Alhaji Dauda Yusif ya ce babu wani cigaba da za a samu muddin babu hadin kai da goyan baya.
Ya kuma ya yabawa kungiyar bisa hada kan al’umma da shugabanni wuri guda.
A jawabinsa, shugaban karamar hukumar Hadejia ta hannun mataimakinsa Abdullahi Usaini Matawalle ya yaba da matakin da kungiyar ta dauka na wayar da kan shugabanni da mabiyansu.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar, Umar Babuga yace mutane 243 suke halartar taron.