Mai ɗaukar hoton gidan Talabijin ɗin Aljazeera ya rasu sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza

Gidan talabijin din na Aljazeera ya bayyana cewa harin jirgi marar matuƙi ne da Isra’ila ta kai a wata makaranta dake Khan Yunis ya kashe Samer Abu Daqqa.

Ma’aikacin na Aljazeera ya ta zubar da jini har ya rasu sakamakon rashin isar masu ceto a makarantar. Aljazeera ta zargi sojojin Isra’ila da hana shigar motar marasa lafiya makarantar da lamarin ya faru da gangan, sai dai sojojin Isra’ilar ba su ce komai kan hakan ba.

Comments (0)
Add Comment