Ma’aikatar Ilimi a Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin kare lafiya da rayukan ɗalibai

Ma’aikatar Ilimi a Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin kare lafiya da rayukan ɗalibai

Ma’aikatar Ilimi a Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wani shiri na ƙara inganta tsaro a manyan makarantu da na sakandare mallakarta da ke ɗaukacin faɗin ƙasar.

Ma’aikatar ilimin ta ce ta ɗauki matakin ne ganin yadda ake samun ƙaruwar ɗaliban da ke mutuwa a faɗin ƙasar, sakamakon harin ƴanbindiga, ko ƙwacen waya, ko wani rikici da ke haɗawa da su ko ɓarkewar annoba.

Babban sakataren ma’aikatar Ilimi ta Najeriya, Dakta Nasiru Sani Gwarzo ya ce za a aiwatar da shirin da aka sake farfaɗo da shi, haɗin gwiwa da ma’aikatar kuɗi da sauran hukumomin tsaron ƙasar don tabbatar da tsare rayuka da lafiyar ɗaliban.

Ya ce ana samun ƙaruwar sace sacen ɗalibai da kai musu hari, inda ya ce za kuma a yi wa ɗalibai bita kan matakan kare kansu daga shiga cikin haɗari.

Comments (0)
Add Comment