Kungiyar kwadago ta NLC ta musanta batun sabawa umarnin kotu dangane da yajin aikin sai baba ta gani da zata tsunduma a ranar Talata mai zuwa.
An bayar da rahotan kungiyar na mayar da martani dangane da kalaman babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a na kasa Lateef Fagbemi daya bayyana matakin nasu a matsayin bujirewa umarnin kotu, kungiyar tana mai cewa hakan bashi da wata makama a kundin tsarin mulki.
Kungiyar tace a shirye take lokaci kawai ake jira domin dakatar da harkkokin aiki yayin yajin aikin da kuma gagarumar zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur da karuwar kudin lantarki, hauhawar farashi da tsadar rayuwa.