Likitar nan da aka yi garkuwa da ita a jihar Kaduna, Dr Ganiyat Popoola ta shaƙi iskar ƴanci bayan shafe kimanin watanni 10 a hannun masu garkuwa da mutane.
Poppola, wadda take aiki a asibitin ido na ƙasa da ke Kaduna, an sace ne a ranar 27 ga Disamban shekarar 2023 tare da mijinta, Nurudeen Popoola wanda sojan sama ne da ɗanuwanta Folaranmi Abdul-Mugniy, amma a watan Maris aka sako mijinta, amma masu garkuwar suka ci gaba da riƙe likitar da ɗanuwan nata.
A watannin baya ne ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa suka shiga yajin aiki saboda nuna rashin jindaɗin su kan gaza ƙwato likitar a hannun masu garkuwa. A jiya Laraba ne dai aka sako likitar da ɗanuwanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga shugaban ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa, Dr Tope Zenith Osundara, wanda ya bayyana cewa ba a biya kuɗin fansa ba.