Kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP sun tabbatar da Wike a matsayin madugun PDP na jihar Ribas

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya samu nasarar tabbatar da matsayinsa na madugun PDP na Rivers bayan da kwamitin zartarwa NWC ta amince da tsagen shi na zaɓaɓɓun shugabannin jam’iyyar PDP na jihar, wanda hakan ya nuna cewa wato Wike ya samu nasara kan gwamnonin PDP.

An yanke wannan shawarar ne a yayin wani taro a hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa da ke Wadata Plaza, Abuja, a ranar Alhamis, ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugaban jam’iyyar, Umar Damagum.

Kwamitin NWC dai ba ta yi taro na tsawon mako uku ba saboda tashe-tashen hankula da ake fama da su musamman tsakanin tsohon gwamnan jihar Ribas Wike da Ƙungiyar Gwamnonin PDP dangane da zaɓen shugabannin PDP na jihar Ribas.

Rikicin ya ɓarke ne a ranar 24 ga watan Agusta inda gwamnonin PDP suka fito ƙarara suka goyi bayan gwamnan jihar Ribas mai ci, Siminalayi Fubara, inda suka yi kira da a sake duba zaɓen shugabannin jihar tare da tabbatar da shugabancin Fubara a jihar.

Wannan goyan bayan ya fusata Wike, wanda a ranar 31 ga watan Agusta ya yi barazanar tayar da tarzoma a jihohin gwamnonin idan suka ci gaba da tsoma baki a harkokin jihar Ribas.

Comments (0)
Add Comment