Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya kaddamar da rabon zakkar da aka tattara a kauyen Masassadi

Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya kaddamar da rabon zakkar da aka tattara a matakin kwamitocin Gunduma a kauyen Masassadi dake gundumar Duma Dumin Toka a karamar hakumar Kafin Hausa.

A jawabinsa shugaban kwamitin Talban Hadejia, Barista Abdulfatah Abdulwahab, ya bukaci alumma dasu rinka bada zakka domin tsarkake dukiyoyinsu.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakin sa kuma babban limamin masarautar Hadejia Dr Yusuf Abdulrahman, ya ce Allah ya albarkaci gundumar Dumadumin Toka da kasar noma da kiwo

Inda ya bayyana muhimmancin bada zakka ga mazauna yankin saboda wadatar da Allah ya yi musu.

A jawabinsa sakataren kwamitin Engineer Isma’ila Garba Barde, ya yabawa kokarin kwamitin zakka na gundumar bisa tattara zakkar kayayyakin amfanin gona ta kimanin naira miliyan bakwai.

Shi kuwa hakimin Dumadumin Toka ta hannun Malam Haruna Idrith Gimba, ya yi godiya ga Allah bisa nasarar da suka samu wajen tattara zakkar.

Comments (0)
Add Comment