Kwamatin kwararru na shugaban kasa kan ambaliyar ruwa ya bada tabbacin lalubo hanyoyin da suka dace domin rage matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa.
Shugaban kwamatin mai kula da jihohin Arewa maso yamma, Dakta Martins Ejauye ya bada tabbacin hakan bayan kammala ziyarar gani da ido wasu wuraren da ambaliyar ruwan Kogi ta shafa a kananan hukumomin Jahun da Kiyawa da Miga da Birnin Kudu da kuma Dutse.
Dakta Martins Ejauye ya ce a matsayin jihar Jigawa da ta ta’allaka akan harkar noma, rage afkuwar ambaliyar zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma da kuma tattalin arzikin al’umma.
A jawabinsa mataimakawa gwamna na musamman kan shigo da al’umma cikin ayyukan gwamnati, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia, ya ce ziyarar kwamatin za ta taimaka musamman wajen daukar matakan da suka dace domin rage yawan afkuwar ambaliyar ruwa a jihar.
A jawabinsa Hakimin Miga kuma Kogunan Dutse, Alhaji Muhammad Ibrahim Garba, ya yabawa kokarin gwamnatin jiha da ta tarayya na kafa kwamitoci da zasu taimaka wajen rage afkuwar ambaliyar ruwa tare da fatan kwamatin zai yi dukkan mai yiwuwa na ganin an rage samun iftila’in ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa.