Rundunar Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta kama mutane 36 tare da kwace kwalbobin Giya guda 647 a fadin Jihar.
Kwamandin Rundunar na Jiha Malam Ibrahim Dahiru ya bayyana haka ga kamfanin dillancin Labarai na kasa (NAN) a birnin Dutse.
Ya ce sunyi nasarar kama wadanda suke tuhumar ne yayin wani sumamen hadin Gwiwa da Jami’an yan sanda da suka gudanar a kananan hukumomin Dutse, da Gumel da Kazaure da ke fadin Jiharnan.
Malam Ibrahim ya ce sun kama mata goma sha 19 wadanda suke tuhuma da laifin karuwanci, ya yin da suka kama maza goma 17 a lokacin kamen da suka gudanar a ranakun 11 da 17 na wannan watan.
Inda ya ce maza 3 da mace 1 daga cikin wadanda suke tuhumar sun kamasu a karamar hukumar Kazaure, ya yin da suka kama 7 a Dutse, 3 maza da kuma 4 mata, haka kuma sun kama mutane 24, 11 maza da 14 mata a karamar hukumar Gumel.
Kwamandan ya ce kwalaban Giya 647 da babura 6 suka yi nasarar kamawa a lokacin kaiwa samamen na karamar hukumar Gumel.
Ya kuma ce sun gabatar da wasu daga cikin wanda suke zargin gaban kotu yayin da suka mika sauran ga jami’an yan sanda domin cigaba da bincike. Daga karshe Kwamandan ya yabawa Jami’an Yansanda bisa yadda suke basu hadin kai, inda ya shawarci ul’umma da su guji aikata ayyukan masha’a wanda ka iya lalata tarbiyar al’umma.