Kusan kashi 65 cikin 100 na talakawan Najeriya na zaune ne a yankin arewacin kasar – Nentawe Yilwatda

Ministan da aka nada a ma’aikatar jin kai da yaki da fatara, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa kusan kashi 65 cikin 100 na talakawa na zaune ne a yankin arewacin kasar, don haka, yankin ya cancanci karin kaso bisa la’akari da bukatun gaggawa.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a gaban Sanatoci domin tantance shi a matsayin minista kuma mamba a majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a jiya Laraba.

Da yake magana kan hanyoyin da ya kamata a bi domin rage radadin talauci a kasar, Yilwatda ya ce, “kashi 65 na talakawa suna zaune a Arewa yayin da kashi 35 ke zaune a Kudu, ya kamata, a yi la’akari da abunda ake bukata a kowace karamar hukuma da jihohi, ta yadda za a raba kudaden shiga duba da jihar da tafi bukata.” Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya zabi Yilwatda a makon da ya gabata domin ya maye gurbin Betta Edu da aka dakatar kuma daga baya aka sallame ta a matsayin ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci.

Comments (0)
Add Comment