Kungiyar ’yan kabilar Igbo ta umarci ’yan kabilar a fadin Najeriya su kaurace wa zanga-zanga

Uwar kungiyar ’yan kabilar Igbo, Ohaneze Ndigbo, ta umarci ’yan kabilar a fadin Najeriya su kaurace wa zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake shirin yi a watan Agusta.

Wata sanarwa da Mazi Okechukwu Isiguzoro ya fitar a ranar Talata ta ce kungiyar Ohaneze Ndigbo ta gargadi masu zanga-zangar.

Ya bayyana cewa a tsawon tarihi, ’yan kabilar Igbo ’yan kabilar Igbo ne suka fi shan wahala bayan duk wata gagarumar zanga-zanga a fadin Najeriya inda suke asarar rayuka da dukiyoyinsu a fadin kasar.

Isiguzoro ya kara da cewa zanga-zangar za ta kara ta’azzara matsalolin tsaro da ake fama da su a yankin Kudu maso Gabas.

Sannan za ta ba da dama ga masu aikata laifuka da makiyan al’ummar Igbo su yi amfani da zanga-zangar wajen haifar da rudani.

Comments (0)
Add Comment