Kungiyar Dalibai ta kasa (NANS) ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin kasa idan gwamnonin jihohin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi ba su janye shawarar rufe makarantu na tsawon makonni biyar domin azumin Ramadan cikin sa’o’i 72 ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar na kasa, Samson Adeyemi, ya fitar a yau, NANS ta bayyana rufe makarantun a matsayin take hakkin dalibai na samun ilimi ba tare da tangarda ba.
Adeyemi ya jaddada cewa wannan mataki zai hana ci gaban karatun dalibai kuma yana nuna wariya ga daliban da ba Musulmi ba.
Ya kara da cewa irin wannan mataki, idan ba a kalubalanta ba, zai zama munanan abin koyi a tsarin ilimin Najeriya.
Duk da haka, kakakin NANS ya bai wa gwamnonin wa’adin sa’o’i 72 don janye wannan doka, yana mai barazanar cewa kungiyar za ta gudanar da zanga-zanga a duk fadin kasar idan hakan bai faru ba.
Ya kuma bukaci sauran masu ruwa da tsaki su mara wa kungiyar baya domin tabbatar da cewa ana kare hakkin dalibai.