Kungiyar matuka ‘yan union ta yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu

kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa ta ‘yan union ta yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga shirye-shirye da manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a kokarinta na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Shugaban kungiyar, Tajudeen Baruwa ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga shugabannin shiyyoyin kungiyar da suka kai masa ziyarar goyon baya jiya a Abuja.

Shugabannin kungiyar na shiyyoyin sun kada kuri’ar amincewa da shugabancin Tajudeen Baruwa tare da yin alkawarin mara baya ga takararsa a karo na biyu a matsayin shugaban kungiyar.

Tajudeen Baruwa ya samu wakilcin mataimakinsa na musamman kan huldar kwadago da masana’antu Abuul Boga.

Tajudeen Baruwa ya ce kungiyar ta yi imanin cewa cire tallafin man fetur zai sa a samu karin kudade domin raya kasa, ciki har da sake gina titunan kasar nan da suka lalace.

Sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga kungiyoyin kwadagon da ke bukatar gwamnati ta samar da hanyoyin rage radadin cire tallafin man ga ‘yan Najeriya.

Comments (0)
Add Comment