Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta ce ta janye yajin aikin da ta fara a ranar 1 ga watan Afrilun da muke ciki.
Shiugaban kungiyar na kasa Dakta Uyilawa Okhuaihesuyi, ya tabbatarwa da manema labarai hakan.
Yace an cimma wannan matsaya ne a wata tattaunawa da aka yi da kwamitin zartarwa na kasa ta intanet da kuma kungiyar a ranar Asabar.
Ya kuma ce “An dakatar da yajin aikin ne har nan da makonni biyu”.
Dakta Okhuaihesuyi ya ce duka manyan jami’ansu da ba a biya ba, za a biya su nan da ranar Litinin.
Ya kara da cewa “Duka mambobinmu za su koma kan tsarin biyan kudin bai daya na IPPIS za kuma a biya su albashinsu