Kungiyar Lauyoyin Mata ta gurfanar da wasu mutane 28 da ake zargi da aikata laifukan fyade

Kungiyar Lauyoyin Mata ta Duniya (FIDA) ta ce ta gurfanar da wasu mutane 28 da ake zargi da aikata laifukan fyade a jihar Yobe a cikin watanni 11 da suka gabata.

Shugabar kungiyar a jihar Yobe, Barista Hannatu Farouk ce ta bayyana hakan ga manema labarai a lokacin shari’ar da ake yi Damaturu babban birnin jihar Yobe .

Ta ce yayin da aka yankewa wasu da ake zargi da aikata fyaden, fiye da mutane 30 sun yi shawarwari ba tare da kotu ba, wanda aka sasanta rikicin. A cewarta, dokar kare yara za ta rage aurar da yara kanana da cin zarafin mata a jihar  ta Yobe.

Comments (0)
Add Comment