Kungiyar Kwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki kan karin kashi 50 cikin 100 na kudin kiran waya

Kungiyar Kwadago (TUC) ta yi barazanar shiga yajin aiki matukar Gwamnatin Tarayya ba ta janye amincewar da ta yi a baya-bayan nan na karin kashi 50 cikin 100 na kudin kiran waya.

Shugaban TUC, Kwamared Festus Osifo ne ya bayyana haka yayin wata hira da gidan Talabijin na Channels a jiya.

Bayan taron majalisar gudanarwar ta na kasa (NAC) a safiyar jiya, kungiyar ta TUC ta yi Allah-wadai da shirin karin kudin kiran wayar da ta ce, ba wai kawai kuskure ba ne, har ma da ganganci da zaluntar ‘yan Najeriya.

Shugaban na TUC ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta magance tushen matsalar.

Comments (0)
Add Comment