Kungiyar kwadago ta masu masana’antu TUC ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin mako guda da biyawa kungiyar dukkan bukatun ta, ko kuma su tsunduma yajin aikin gama gari kamar yadda kungiyar kwadago ta NLC tayi barazanar shiga.
Shugaban kungiyar TUC Festus Osifo yace kungiyar tasu tayi kokarin ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dangane da wasu bukatu da suke son a biya musu.
Ministan kwadago Simon Lalong ya tabbatarwa kungiyar cewa gwamnatin tarayya tana iya bakin kokarin ta domin magance matsalolin kungiyar.
Sawaba radio ta rawaito cewa dukkanin bangarorin biyu sun cimma matsayar biya kungiyar bukatun ta cikin makonni 2.