Kungiyar Fityanul Islam ta nesanta kanta game da zanga-zanga da ake shirin yi a fadin Najeriya

Kungiyar Fityanul Islam ta nesanta kanta game da shirin zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a fadin Najeriya wacce aka shirya gudanarwa daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Augusta a fadin kasar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, ustaz Sani ibn Salihu wacce shugabanta Sheikh Dakta Muhammad Arabi AbulFathi ya sanya wa hannu a ranar 15 ga watan yulin 2024

Kungiyar ta yi nuni da cewa, irin wannan gagarumin mataki da ake shirin dauka bai cika haifar wa al’umma alheri ba.

“Kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya ta nesanta kanta da irin wannan gagarumin mataki na zanga-zanga domin za a iya samun marasa kishin kasa su tayar da tarzoma da ka iya haifar da rugujewar bin doka da oda.

Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta sake bitar duk wasu tsare-tsare, musamman wadanda suka jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyaciyar rayuwa.

Comments (0)
Add Comment