Ana kokarin amincewa da kudirin dokar da ke neman kara yawan kananan hukumomin Jihar Legas daga 20 zuwa 57, bayan da ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai a jiya Laraba.
Wannan kudiri, wanda yana daga cikin kudirori 42 na gyaran kundin tsarin mulki da ‘yan majalisa suka amince da su, zai daukaka karin gundumomin raya yankuna guda 37 zuwa cikakkun kananan hukumomi. Kudirin, wanda ya tsallake karatu na biyu a zaman majalisa na ranar Laraba, ‘yan majalisa da suka dauki nauyin gabatar da shi sun hada da James Abiodun Faleke (Mazabar Tarayya ta Ikeja), Babajimi Benson (Mazabar Tarayya ta Ikorodu), da Enitan Dolapo Badru (Mazabar Tarayya ta Legas Island I), tare da goyon bayan wasu ‘yan majalisa 19.