Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Legas ta yi watsi da bukatar Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, na hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani.

Mai shari’a Polycarp Terna Kwahar, wanda ya karanto hukuncin a madadin kwamitin alkalan uku, ya bayyana matsayar kotun. Sauran alkalan, Mai shari’a Mohammed Mustapha da Mai shari’a Paul Bassi, sun goyi bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Ikeja ta yanke a ranar 10 ga Janairu, 2021.

A watan Yuli na 2010, Mista Falana ya gurfanar da Gwamnatin Tarayya a gaban kotun, inda ya nemi, kotu ta ayyana cewa ‘yan Najeriya suna da ‘yancin samun kiwon lafiya mafi inganci kamar yadda doka ta tanada. 

Ya kuma bayyana cewa gazawar gwamnati wajen gyara da samar da kayan aiki a asibitocin gwamnati ya sabawa ‘yancin kare lafiyar ‘yan kasa da tabbatar da cewa suna samun kulawar lafiya lokacin da suka yi rashin lafiya.

Falana ya nemi kotu ta umarci gwamnati da ta gyara tare da samar da kayan aiki a asibitocin kasar, da kuma hana jami’an gwamnati zuwa asibitocin ketare domin duba lafiyarsu ko samun magani da kuɗin gwamnati.

Bayan kotun sauraron ƙorafin, ta yi watsi da karar, tana mai cewa samar da wadatattun cibiyoyin kiwon lafiya ba abu ne da za a iya tilasta wa gwamnati ta hanyar kotu ba, bisa la’akari da sashe na 6 (6) (C) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment