Kotun ƙoli ta Najeriya ta yi watsi da hukuncin wata kotun ɗaukaka ƙara ta ƙasar wadda ta ce madugun ƴan awaren Ipob, Nnamdi Kanu ba zai fuskanci shari’a ba kasancewar an kama shi ne ba bisa ƙa’ida ba.
Saboda haka nan alƙalan kotun suka ce za a ci gaba da yi wa Kanu shar’ia.
A yau ne kotun ta yanke wannan matsaya kan Nnamdi Kanu, wanda ke da mabiya a ciki da wajen Najeriya.
Shari’ar Nnamdi Kanu ta baya-bayan nan ta faro ne tun daga shekarar 2021, daga Babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Wannan dai shi ne kat, game da batun ko za a saki Nnamdi Kanu ko a’a, kasancewar ba za a iya ɗaukaka ƙara ba.
Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
A shekarar 2015 ne aka kama Mr Kanu amma ya tsere daga Najeriya a 2017 bayan an bayar da shi beli.
Ya kasance a tsare tun 2021 lokacin da aka tasa ƙeyarsa daga Kenya domin fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci.
A watan Oktobar bara ne, wata kotun ɗaukaka ƙara ta bayar da umarnin a saki Mista Kanu inda ta ce akwai kura-kurai a shari’ar.
Sai dai gwamnati ta sake shigar da ƙara inda ta ce Kanu barazana ce ga tsaron Najeriya.
Wasu shugabannin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun nemi a saki Kanu. A zaman da ta yi na ƙarshe, ranar 5 ga watan Oktoba, 2023, kotun ƙolin ta ajiye ranar 15 ga watan Disamba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci.