Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin kisa saboda kashe kawunsa a Hadejia

Wata Babban Kotun Jihar Jigawa wanda take zaman ta a nan Hadejia a jiya ta yankewa wani Mai suna Magaji Husseini Lushe, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samun sa da laifin kashe kawunsa.

Da yake yanke hukunci Alkalin Kotun Mai Shari’a Ado Yusuf Birnin Kudu, ya ce Kotun ta samu mutumin wanda mazaunin Rigar Dadi Lamido dake Karamar hukumar Kirikasamma ne da laifin kashe kawun sa Muhammad Alhaji Amadu da wuka.

Alkalin Kotun ya ce mutumin da ake zargin ya amsa laifinsa, a lokacin da ya bayyana a gaban Kotun, inda ya ce ya yi kisan ne

Comments (0)
Add Comment