Kotu ta wanke Naira Marley daga zargin hannu a mutuwar Mohbad

Kotun majistare da ke zama a Sabo, da ke unguwar Yaba a jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad.

Mai shari’a Ejiro Kubenje, wanda ya karanta hukuncin ya ce babu wata ayar tambaya kan mutanen biyu game da rasuwar Mohbad.

Haka nan ma kotun ta sallami Oodunni Ibrahim, wanda ake kira Primeboy da tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde.

Sai dai hukuncin ya ce za a gurfanar da ma’aikaciyar jinyar da ta kula da Mohbad gabanin mutuwarsa, wato Feyisayo Ogedengbe, da ɗaya daga cikin abokan marigayin, Ayobami Sadiq bisa tuhumar su da sakaci, wanda ya kai ga mutuwar matashin mawaƙin.

Comments (0)
Add Comment