Kotu Ta Dakatar Da Natasha Da Akpabio Daga Yin Hira Da ‘Yan Jarida

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarni ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio da wasu, da su daina bayar da hira ko wallafa bayanai kan karar da ke gaban kotu a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta, har sai an kammala sauraren shari’ar.

Mai shari’a Binta Nyako, wacce ta karɓi jagorancin sauraren karar daga hannun Mai shari’a Obiora Egwuatu, ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin tabbatar da adalci da guje wa tasirin waje kan shari’ar.

An sauya alƙalin ne bayan da Egwuatu ya janye daga karar bisa zargin son kai da wasu ke masa dangane da lamarin Akpabio.

Comments (0)
Add Comment