Ministan yada labarai da al’adu na kasa Lai Muhammad ya bayyana cewa, ko shugaban kasa Muhammadu buhari bazai iya cewa, zai kawo karshen yan fashin daji ba a karshen shekara mai zuwa ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin dayake zantawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, a lokaci da aka tambaye shi ko zasu iya magance matsalar rashin tsaro kafin karewar wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Ya kara da cewa, shugaban kasa Muhammadu babu wani abu daya rage masa yanzu haka.
Saidai idan karya yan Nigeria suke bukata ayi musu.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Litinin ya bayyana cewa, shugaba Buhari babu wani abu da zai iya yi a bangaren tsaro, saboda yayi iya abinda zai iya.
Amma Lai ya kara da cewa, karfafawa jami’an tsaro gwaiwa da cigaba da matsa lamba zai kara karfafa tsaro a fadin kasar nan.