Alkaluman da Ofishin Kula da Bashi ya fitar ya nuna cewa basussukan da ake bin kasarnan ya karu da Naira Biliyan 560.
A cewar ofishin, jimillar gabadaya bashin da ake bin kasar, ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2019, ya kai Naira Tiriliyan 24 da Biliyan 900, idan aka yi la’akari da yawan bashin, Naira Tiriliyan 24 da Biliyan 300 zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2018.
Takardar alkaluman bashin da ofishin ya fitar ya nuna cewa anyi amfani da tsarin canjin kudi na Babban Bankin CBN akan Naira 306 da Kobo 95 akan kowace Dalar Amurka, wajen canja yawan bashin cikin gida zuwa Dalar Amurka.
Alkaluman sun nuna cewa gabadaya bashin waje yakai Naira Tiriliyan 7 da Biliyan 800 (Kimanin Dalar Amurka Biliyan 25 da Miliyan 600), yayinda bashin cikin gida ya kai yawan Naira Tiriliyan 17 (Kimanin Dalar Amurka Biliyan 55 da Miliyan 600).
Bashin waje shine ya debi kaso 31 da digo 5 cikin 100, yayinda bashin cikin gida ke da kaso 68 cikin 100.
A cewar ofishin kula da bashin, karuwar bashin ya ta’allaka ne akan karuwar bashin cikin gida wanda ya karu da Naira Biliyan 458 da Miliyan 363.
Hauhawar bashin ya samu ne a bashin cikin gida na Gwamnatin Tarayya, Jihohi da kuma Birnin Tarayya Abuja.
Bashin waje ma ya karu da Naira Biliyan 101 da Miliyan 646 a cikin tsawon lokacin.