Kimanin ƙunzugun yara (Famfas) 13,350 ne suka ɓata a wani asibiti da ke jihar Kebbi

Hukumar yaƙi da almundahana ta ICPC a Najeriya ta ce za ta binciki batun ɓacewar ƙunzugun yara da aka fi sani da Famfas kimanin 13,350 a ƙaramin asibitin shan magani da ke Sambawa a jihar Kebbi.

Shugaban hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin taron da hukumar da shirya a Abuja.

Ya ce hukumar za ta yi bincike domin gurfanar da waɗanda ke da hannu a ɓacewar famfas ɗin.

Shugaban hukumar ya ce al’ummar Sambawan ne suka kai wa hukumar ƙorafin ɓacewar famfas ɗin da aka tanada domin tallafa wa masu juna biyu da jaririn da ake haifa a asibitin.

“Bincikenmu na farko ya nuna mana cewa yawan ƙunzugun da suka ɓace a asibitin ya kai 13,350, to amma binciken hukumar lafiya a matakin farko ta jihar Kebbi ya nuna adadin 3,466 ne”, in ji Adamu.

Ya ce akai mutum biyu mace da na miji da ke aiki da ƙaramin asibitin na Sambawa da ake zargi da hannu a ɓacewar tarin ƙunzugun.

Comments (0)
Add Comment