Kasar Zimbabwe ta kawo karshen yanke hukuncin kisa

A hukumance ƙasar Zimbabwe ta kawo karshen yanke hukuncin kisa, bayan shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya rattaɓa hannu kan dokar.

A yanzu za a maye gurbin hukuncin kisa da zaman kaso na har abada, kuma mutane kusan 60 ne za su fara cin gajiyar dokar a ƙasar.

An shafe gwamman shekaru ana ta kai ruwa rana kan batun hukuncin kisa, amma kotuna suka ci gaba da yanke hukuncin da suka haɗa da samun mutum da laifin kisan kai da cin amanar ƙasa da ayyukan ta’addanci.

Kungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ta yi maraba da wannan doka da ta ce mai cike da tarihi ce. 

Comments (0)
Add Comment