Kasar Rwanda ta halarta bulaguro zuwa kasar sa ba tare da biza ga daukacin ‘yan Afirka ba

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya gabatar da shirin bulaguro zuwa kasar sa ba tare da biza ga daukacin ‘yan Afirka ba, lamarin da ya sa kasar Rwanda ta kasance kasa ta hudu a Afirka da ke yin hakan.

Shugaba Kagame ya ce babu kuskure game da hakan, kuma duk wani ba’afrike na iya hawa jirgi zuwa Rwanda a duk lokacin da ya ga dama kuma ba zai biya komai ba don shiga kasar.

Yanzu haka Rwanda ta hade da Seychelles, Gambia da Benin, kasashen Afirka da ke ba da izinin shiga ba tare da biza ba ga dukkan ‘yan Afirka.

A wannan makon, shugaban kasar Kenya William Ruto ya sanar da cewa kasar za ta kawo karshen bukatuwar biza ga dukkan masu ziyara a Afirka nan da shekarar 2024. Haka kuma kasashen Afirka da dama sun kulla yarjejeniya da kasashen biyu na tafiye-tafiye ba tare da biza ba, na baya-bayan nan sune kasar Ghana da Afirka ta Kudu, da Uganda da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

Comments (0)
Add Comment