Gwamnatin kasar Jamus ta sanar da kara bai wa Najeriya tallafin Yuro miliyan 24 da saura kasashen yankin Sahel da na yankin tafkin Chadi da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin Jakadancin Jamus da ke babban Birnin tarayya Abuja.
Gudunmawar ta baya-bayan nan ta kai jimillar kudaden tallafin jin-kai da Jamus ta bayar a yankunan Sahel da tafkin Chadi zuwa Yuro miliyan 100.
Ambaliya a yankunan Sahel da tafkin Chadi, ciki har da Nijeriya sun haddasa gagarumar matsalar jin-kai.
Baya ga gudunmawar jin-kai, Jamus ta sha bai wa yankin tafkin Chadi gudunmawa a shirye-shirye daban-daban, da suka shafi hadin kai da ci gaba, wadanda darajarsu ta kai miliyoyin Yuro.