Ministan ƙasashen waje na Isra’ila, Israel Kartz ya ce Isra’ila “ba ta maraba” da sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres kuma an haramta masa shiga ƙasar.
Israel Katz ya ce an cimma wannan matsaya ne bisa la’akari da gazawar Antonio Guterres ta ƙin yin kakkausan suka ga harin da Iran ta kai wa Isra’ilar ranar Talata.
Ya kuma zargi shugaban na Majalisar Ɗinkin Duniya da “nuna ƙiyayya ga Isra’ila” da “goyon bayan ta’addanci da fyaɗe da kisan jama’a.
“Tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya ba zai taɓa manta wa Guterres ba a matsayin gurɓatacce .”
A jiya ne dai sakatare janar na Majalisar Ɗinkin ta Duniya ya alawadai da abin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya inda kuma ya yi kira da cimma tsagaita wuta.